11 Satumba 2025 - 13:12
Source: ABNA24
Araqchi Ya Ziyarci Masallacin "Jami’iz-Zaytouna" Inda Ya Gana Da Babban Mufti Na Tunisia

Babban Mufti na Jamhuriyar Tunisiya, yayin da yake bayyana jin dadinsa da halartar ministan harkokin wajen kasar a masallacin Jami’iz-Zaytouna, ya yi bayani kan tarihin wannan masallaci da matsayinsa da kuma muhimmancinsa wajen yada addinin Musulunci na rahama a kasashen Tunisiya da Arewacin Afirka da ma daukacin kasashen musulmi baki daya.

Ministan harkokin wajen kasar Iran wanda ya je wannan kasa domin tuntubar wasu manyan jami'an gwamnatin kasar Tunusiya, ya gana tare da tattaunawa da Sheikh Hisham Mahmoud, babban Mufti na kasar Tunusiya a yammacin ranar Laraba, wanda ya yi daidai da zagayowar ranar da aka haifi Manzon Allah (S.A.W), a lokacin da ya halarci masallacin "Jami’iz-Zaytouna".

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: a yayin wannan ziyara, ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi ya taya al'ummar kasar Tunisia murnar zagayowar ranar haihuwar manzon Allah (SAW), inda ya jaddada wajabcin hadin kan dukkanin musulmi bisa koyarwar manzon Allah mai girma da daukaka, yana mai ishara da ci gaba da laifuffukan da gwamnatin sahyoniyawa ta ke yi a Gaza da kuma fadada fagagen ayyukan ta’adancin wannan haramtacciyar Isra'ila a yankin na Gaza, da kuma ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri a yankin Gaza da ke yammacin Asiya wand domin tunkarar wannan fadadawar akwai bukatar hadin kai da hadin gwiwar ga al'ummar musulmi.

Babban Mufti na Jamhuriyar Tunisiya, yayin da yake bayyana jin dadinsa da halartar ministan harkokin wajen kasar a masallacin Jame’iz-Zaytouna, ya bayar da bayani kan tarihin wannan masallaci da matsayinsa da muhimmancinsa wajen yada addinin musulunci na rahama a kasar Tunisiya da arewacin Afirka da ma daukacin kasashen musulmi baki daya.

Masallacin Jame’iz-Zaytouna na daya daga cikin tsofaffin masallatai a kasar Tunisia mai dogon tarihi da matsayi na tarihi, wanda aka gina a shekara ta 79 bayan hijira, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen yada ilimin addinin musulunci tsawon tarihinsa.

A cikin taron manema labarai da ya yi, ministan harkokin wajen kasar Iran, yayin da yake magana kan yarjejeniyar da hukumar makamashin nukiliya ta kasar ta yi, ya ce: Hukumar ta amince da cewa, abin da ke faruwa a yanzu ya canza, kuma akwai bukatar wani sabon tsarin hadin gwiwa.

A cewar Sayyid Abbas Araqchi wanda ya je kasar Tunisia a yammacin Laraba a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da ministan harkokin wajen kasar Tunisiya Mohammed Ali Nafti ya yi: Muna gode wa kasar Tunisiya bisa tsayin daka da nuna damuwa wajen yin Allah wadai da cin zarafin da gwamnatin sahyoniyawa da Amurka suka yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Ya ci gaba da cewa: Matsayin Tunusiya na yin Allah wadai da wannan wuce gona da iri da kuma bayyana goyon baya da hadin kai ga al'ummar Iran wani matsayi ne bayyananne kuma tabbatacce. Dangane da haka ne Araqchi ya jaddada cewa: Ziyarar da shugaban kasar Tunusiya ya kai kasar Iran a bara domin halartar jana'izar shahidan Raisi da ganawarsa da Jagoran juyin juya halin Musulunci a kasar Iran wani lamari ne da ya kawo sauyi kan alakar kasashen biyu. A yayin da yake ishara da tattaunawar da ya yi da ministan harkokin wajen kasar da kuma shugaban kasar Tunisia, Araqchi ya bayyana cewa: A yau mun yanke shawarwari masu kyau dangane da yadda za a fadada dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta fuskar cinikayyar kasuwanci, likitanci, Ilimi da al'adu, kuma an amince da cewa nan ba da jimawa ba za a gudanar da kwamitin tattalin arzikin kasashen biyu a birnin Tehran. Har ila yau ya bayyana cewa, a yayin wadannan shawarwarin, mun tattauna kan hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin Sahayoniya ta kai kan kasashe daban-daban na yankin, ciki har da harin da gwamnatin ta kai kasar Qatar a jiya, inda ya ce: Barazanar gwamnatin yahudawan sahyoniya ita ce babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin, kuma tunkarar ta na bukatar yanke yunkuri na bai daya a yankin. Da yake bayyana cewa muna yin Allah wadai da harin wuce gona da iri da gwamnatin sahyoniyawan ta yi wa kasar Qatar a jiya tare da bayyana goyon bayanta ga gwamnati da al'ummar kasar Qatar, ya ci gaba da cewa: Mun yanke shawarar ci gaba da tuntubar juna ta fuskar siyasa a wannan fanni.

Your Comment

You are replying to: .
captcha